Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Hukumomin Gibraltar sun nemi Birtaniya ta tura dakaru domin yin barazana ga Spain

Babban Ministan yankin Gibralter ya yi kira ga Birtaniya da ta aika da mayakan ruwanta domin yin barazana ga kasar Spain da ta aika da jiragen ruwan ta zuwa yankin. 

Wani jirgin ruwan Spain a ruwan Gibratlar
Wani jirgin ruwan Spain a ruwan Gibratlar REUTERS/Jon Nazca
Talla

Fabian Picardo ya zai goyi bayan duk wani mataki da zai sa Spain ta kaucewa bijirewa odar da aka bata na jirgin ruwan ta ya fice daga yankin.

Tun bayan hawan Fira Ministan Mariono Rajoy karagar mulki Spain a watan Disambar 2011 Spain ta ke mamaye yankunan ruwan dake Gibraltar akai akai.

“Muddin ba a taka musu birki ba za su ci gaba da yin hakan idan dai har suna kan mulki.” Inji Picardo.

Kasar Spain dai ta mikawa Birtniya mallakar Gibraltar a shekarar 1713 amma tana ikrarin a mayar mata da yankinta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.