Faransa
Jirgi dauke da gawar Philippe Verdon ya isa Paris na kasar Faransa.
A yau laraba, an dawo da gawar Philippe Verdon a birnin Paris, wato daya daga cikin Faransawa 7 da aka sace a kasar Mali, sannan aka tsinci gawarsa a cikin makwannin da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Talla
Shi dai Verdon an sace shi ne a watan Nuwambar shekara ta dubu biyu da 11 a kasar Mali, kuma kwanaki kadan bayan hakan ne Kungiyar AQMI reshen kungiyar Alqa’ida a arewacin Afirka ta ce ita ce ta sace shi.
To sai dai a cikin watan Maris da ya gabata, kungiyar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa ta kashe Verdon dan kimanin shekaru hamsin da uku a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu