Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ce kasar da masu yawon buda ido suka fi ziyarta a duniya

Tare da samun karin masu yawon bude daga kasashen ketare, Faransa, a cikin shekarar da ta gabata, ta kasance a sahun gaba ta fannin karbar masu yawon bude a duniya fiye da shekara ta 2011 inda mutane milyan 81 suka ziyarci kasar.

Dutsen Mont-Saint-Michel, daya daga cikin wuraren da masu yawon buda ido ke shawa a Faransa
Dutsen Mont-Saint-Michel, daya daga cikin wuraren da masu yawon buda ido ke shawa a Faransa RFI/Bruno Faure
Talla

Duk da matsaloli na siyasa da kuma na tattalin arziki da ke addabar na duniya, to amma hakan bai shafi bangaren yawon buda ido na kasar ta Faransa ba kamar dai yadda wannan rahoto ya nuna,

‘Yan asalin kasashen nahiyar turai sun kasance a sahun gaba wajen zuwa faransa sakamaakon yadda kasar ke jan hankulan baki a cikin shekarar ta 2012, kuma yawansu ya karu da kimanin kashi biyu cikin dari daga Turai, yayin da aka sami baki daga Asiya da yawansu ya karu da akalla kashi 9.9 bisa dari a cewar rahoton.

Daga kasar China kawai an samu ‘yan yawon bude da ido su milyan daya da dubu dari hudu da suka ziyarci Faransa, to sai dai Jamusawa ne ke sahun gaba wajen ziyartar faransa, inda yawansu ya kai milyan 12 da dubu dari biyu.

Daga karshe dai Faransa ta samu Euro bilyan 35 da digo 8 a matsayin kudaden shiga daga masu yawon buda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.