Isa ga babban shafi
Faransa

Matsalar Na’ura ta haifar da hadarin jirgin kasa a Faransa

Mahukuntan kula da jiragen kasa a Faransa sun ce Hadarin jirgin da aka samu bayan da jirgin ya kaucewa titinsa ya faru ne sakamakon matsalar na’ura wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida tare da raunata wasu da dama.

Hadarin jirgin kasa da aka samu a Brétigny-sur-Orge a kasar Faransa
Hadarin jirgin kasa da aka samu a Brétigny-sur-Orge a kasar Faransa AFP/KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Mahukuntan sun ce hadarin ya faru ne sakamakon matsala da aka samu daga na’urorin canza wa jirgi hanya.

Tuni dai Ministan sufurin Faransa Frederic Cuvillier ya yi watsi da zargin matsalar ta faru ne daga matukin jirgin wanda Ministan yace ya ga kokarinsa da ya karkatar da jirgin wanda hakan yasa ba a samu jikkata da yawa ba.

Akalla Mutane 30 ne suka samu rauni sakamakon hadarin, kuma 8 daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya ziyarci inda wannan hatsari ya faru domin jajantawa jama’a.

Rahotanni  sun tabbatar da cewa jirgin ya kaucewa hanyarsa ne, lamarin da ya yi sanadiyyar kwancewar taragonsa 4 wanda ke dauke da fasinjoji a cikinsu.

Jirgin ya fito ne daga birnin Paris a ranar Juma’a akan hanyarsa zuwa Limoges amma jirgin ya samu hadari ne a Bretigny-sur-Orge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.