Isa ga babban shafi
Ireland

An raunata ‘Yan sanda 47 a Arewacin Ireland

Wasu ‘Yan sanda 47 sun samu raunuka, a wani rikicin addini da ya auku a Arewacin kasar Ireland a yayin da ake gudanar da wani fareti.

Taswirar kasar Ireland
Taswirar kasar Ireland www.lonelyplanet.com
Talla

Hukumar ‘Yan sandan kasar wacce ta tabbatar da hakan, ta ce mabiya bangaren Protestant sun yi yunkurin hana wani fareti da mabiya bangaren Katolika ke kokarin gudanarwa, inda su ka abkawa ‘Yan sandan a yayin da su ke kokarin shiga tsakani.

Dukkanin bangarorin biyu ne dai su kai hari kan ‘Yan sandan da kwalabe cike da man fetur da kayayyakin wuta.

A cewar hukumar ‘Yan sandan, an kai hudu daga cikin wadanda su ka samu raunka asibiti a yayin da wasu 43 su ka sami kananan raunuka.

“Ina bakin ciki da irin wannan hari da aka yi kan ma’ikatana”, inji babban ‘Yan sanda Arewacin Ireland, George Clarke.

Ya kara da cewa “ duk wata sa’a da aka yi rikici na saka rayuka cikin hadari tana kuma rage yarda a tsakanin al’umarmu, kana ana asarar kudaden da ya kamata a ce an kashe su a sashin ilmi da kiwon lafiya”

Ya kuma kara da cewa, tashin hankali ba ya kasancewa mafita ga duk wata damuwa.

Akalla mutane 3,500 su ka mutu a rikicin daban daban a shekaru da dama da su ka wuce a rikicin da kan auku tsakanin ‘Yan katolikan Arewacin kasar da kuma ‘Yan Protestants.

An dai taba yin wata yarjejeniyar sulhu a shekarar 1998 bayan wani rikicin da aka tafka da barazanar hare-haren bam.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.