Isa ga babban shafi
Ireland

Yunkurin Cire Fira Ministan Ireland Taci Tura

Wani yunkuri na kwace mukamin Shugaban Jamiyyar dake mulkin kasar Ireland daga hannun Fira Minista Brian Cowen taci tura.Ministan harkokin kasashen waje na kasar yake kan gaba wajen nuna kyamar ganin Fira Ministan na rike da mukamin na shugaban Jamiyyar.Jiya ne Shugaban Jamiyyar Cowen yace ya dace a jefa kuria ko ana bukatar ya cigaba da zama Shugaban jamiyyar ta Fianna Fail, bayan yaki amincewa daya sauka kamar yadda wasu ke bukata.Tun cikin shekarar data gabata ne dai ake ganin Mukamin Fira Ministan nata tangal-tangal, lokacin da kasar ta nemi rance daga Asusun bada Lamuni na duniya, na kudin Turai euro biliyan 85, gashi kuma akwai rade-radin yana wani taro da Shugabannin bankunan kasar da suka durkushe. 

Fira Ministan Ireland Cowe Kuma Shugaban jamiyyar Fianna Fail
Fira Ministan Ireland Cowe Kuma Shugaban jamiyyar Fianna Fail rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.