Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Kowace rana tana da muhimmaci ga kasar Girka-Merkel

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, tace, kowace rana tana da muhimmanci ga kasar Girka, a kokarin da kasar ke yi wajen bin matakan da ta yi alkawarin za ta bi don kaucewa ficewa daga yankin kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Shugabar Gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel tare da Firaministan kasar Girka Antonis Samaras
Shugabar Gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel tare da Firaministan kasar Girka Antonis Samaras REUTERS/Thomas Peter
Talla

Angela Merkel, tace tuni an riga an fara cire rai tun shekaru biyu da rabi da suka wuce akan kasar Girka, game da ci gaba da kasancewar cikin kasashe masu amfani da kudin Euro, saboda matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Sai dai Merkel ta jaddada cewa, akwai bukatar a jira a ga rahotan da masu bin kasar ta Girka bashi za su fitar a watan gobe.

A kwanakin baya, rahotanni sun nuna cewa, Ministan tattalin arzikin kasar Jamus, Philip Roasler, ya nuna shakkunsa akan ci gaba da kasancewar kasar ta Girka a yankin.

Masana suna ganin idan aka sami rahotanni masu armashi, daga Kungiyar Tarayyar Turai da IMF, da kuma Babban Bankin Tarayyar Tura, hakan zai ba kasar damar samun bashin kudin euro Biliyan 31.5

A satin da ya gabata ne, Merkel, ta karawa kasar Girka kwarin gwiwa inda ta nuna akwai bukatar kasar ci gaba da kasancewa cikin kungiyaar kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Merkel ta yi alkawarin Jamus za ta taimakawa kasar a yayin da ta yi wani zama tare da Firaministan Girka Anthonio Samaras.

Kokarin ceto tattalin arzikin kasar Girka ya dogara ne akan kasar Jamus wacce ta fi kowace kasa karfin tattalin arziki a cikin kasashen masu amfani da kudin euro.

Amma sai babbar kotun kasar ta yanke hukunci akan irin matakan da ita Jamus din za ta dauka wajen Tunkarar matsalar tattalin arziki da ke addabar yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.