Girka
Firaministan Girka ya nemi karin lokaci don kaddamar da sauye sauye
Firaministan kasar Girka Antonis Samaras yace kasarsa tana bukatar karin lokaci domin kaddamar da sabbin sauye sauyen matakan tsuke bakin aljihun gwamnati. A cikin makon nan ne Samarar zai gana da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa François Hollande.
Wallafawa ranar:
Talla
Samaras yace gwamnatinsa tana bukatar Lokaci domin sassauta tasirin kasafin kudi ga al’ummar kasar Girka. Shugaban yace yanzu ba su bukatar wani karin tallafi illa bukatar ci gaban tattalin arziki tare da ganin kudaden shigar kasar sun inganta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu