Isa ga babban shafi
Girka

Firaministan Girka yana neman karin shekaru biyu

Fira Ministan kasar Girka Antonis Samaras na shirin neman bukatar karin shekaru biyu game da tsarin tayar da komadar tattalin arzikin a taron da zai yi makon gobe da Shugabannin kasar Jamus da Faransa.

Firaministan kasar Girka  Antonis Samaras
Firaministan kasar Girka Antonis Samaras REUTERS/Yorgos Karahalis
Talla

Kamar yadda mujallar Financial Times ta bayyana Firaministan kasar zai nemi a yi tsarin takaita kashe kudade na tsawon shekaru hudu maimakon biyu.

A makon gobe ne Shugaban zai gana da Ministocin kudi na kasashe masu amfani da kudaden Euro kafin ya tafi Berlin na kasar Jamus ranar Juma’a, inda zai gana da Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel, ranar Asabar kuma ya mika Paris na kasar Faransa domin tattaunawa da Shugaban kasar Faransa Francois Hollande.

Hukumomin kasar Girka ba su gabatar da wadannan bayanai ba, amma kuma wani mai Magana da yawun Shugaban Gwamnatin Jamus yace matsayin Jamus game da tattalin arzikin Girka bai canza ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.