Isa ga babban shafi
Girka

Hollande da Merkel za su tattauna akan makomar Girka a yankin kasashe masu amfani da Euro

Shugabannin kasashen Jamus da Faransa, Angela Merkel da takwaranta Francois Hollande za su tattauna akan makomar kasar Girka a yankin kasashen masu amfani da kudin euro a nahiyar Turai.Wannan tattaunawa za ta kasance a daidai lokacin da kasar ta Girka ke nema a kara mata lokaci domin ta killata zamanta a cikin kasashen masu amfani da kudin euro.  

Shugabar kasar Jamus, Angela Merke tare da takwaranta, shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Shugabar kasar Jamus, Angela Merke tare da takwaranta, shugaban kasar Faransa, Francois Hollande AFP PHOTO / POOL / FRANCOIS NASCIMBENI
Talla

Shugabannin biyu za su daidaita matsayar su ne a tattaunawar inda daga baya za su gana da Firaministan kasar ta Girka, Antonis Samaras a cikin satin.

Merkel na da ra’ayin kasar ta Girka da kada ta fice da cikin kasashe masu amfani da kudin na euro.

Za ta gana a gobe tare da Samaras kana shi kuma Hollande zai gana da shi a ranar Asabar.

A wata hira da shugaba Samaras ya yi da ‘Yan jarida, y ace kasar ta Girk ana bukata dan wani lokaci domin ta shimfida matakan tsuke aljihu domin share fagen samun kudaden ceto kasar anan gaba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.