Isa ga babban shafi
Faransa

Sharhin Jaridun Faransa: 5 ga watan Yuni 2012

Sabon hoton Shugaban Faransa, François Hollande, da zaben ‘Yan Majalisu da batun kadaici a Faransa da maganar rikicin Mali su ne batutuwan da suka mamaye jaridun Faransa a ranar 5 ga watan Yuni shekarar 2012.

Wasu Jaridun kasar Faransa dauke da labaran zaben shugaban kasa
Wasu Jaridun kasar Faransa dauke da labaran zaben shugaban kasa Sergueï Dmitriev / RFI
Talla

Kafin zaben ‘Yan Majalisu a Faransa jaridar Libération ta buga babban labari ne da tambayar “ko Jam’iyyar gurguzu zata sha kaye a zaben”? shafin Farko na jaridar kuma ya buga labari game da sabon hoton shugaban Faransa François Hollande, wanda ya dauka domin amfani da shi a makarantu da ma’aikatun gwamnati da Bankunan Faransa. Hollande ya dauki hoton ne kamar yadda tsohon shugaban kasa Jacques Chirac ya dauka a fadar shugaban kasa ta Elysée a birnin Paris.

Jaridar Aujourd'hui en France, ita ma ta buga labari ne game da sabon hoton shugaban, inda tace Hoton ya nuna shugaban kamar yana tafiya a saman hanya kuma hoton ya yi dai dai da matsayin shugaban kasa.

Jaridar Libération ta yi nazari ne game da zaben ‘Yan Majalisu. Jaridar tace Jam’iyyar Hollande da masu ra’ayin kasa suna da yakinin samun yawan rinjayen kujeru a majalisar bayan wani sakamakon ra’ayin jama’a da aka gudanar wanda ya nuna Jam’iyyar Hollande ta samu rinjaye da kashi 62. Sai dai Jaridar ta yi gargadin magoya bayan Jam’iyyar NF zasu iya kauracewa zaben.

Yawancin Jaridun Faransa sun yi nazari akan ‘Yan takarar da Faransawa mazauna kasashen waje zasu zaba.

A nata bangaren Jaridar Le Monde, ta bayyana damuwa ne game da rikicin Mali tare da fargabar Mali zata iya rikedewa kamar Somalia. Jaridar dai ta yi sharhi game da barakar kawancen ‘Yan tawayen Azawad da kungiyar musulmi ta Ansar Dine masu fafutikar kafa shari’a a Arewacin Mali.

Jaridar tace kawai alamar Tambaya akan asalin wanda ya jagoranci juyin mulkin a ranar 22 ga watan Maris.

Jaridar Le monde dai ta samu zantawa da Nina Walet Intalou mace tilo daga MNLA da ke zama a Nouakchott inda ta yi kira ga kasashen Duniya magance barakar Mali.

Jaridar Katiloka ta La Croix kuma ta yi bayani game da zaman kadaici a Faransa da yara kanana ‘Yan shekaru Biyar ke fama a cikin kasar.

Jaridar ta kwatanta mizanin kadaici a Faransa da kuma kasar Japan inda kadaici ya zama rayuwar mutanen Japan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.