Isa ga babban shafi
Rasha-Syria-Faransa-Jamus

Jamus da Faransa sun nemi Rasha katse hulda da Syria a ziyarar Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin zai kai Ziyara zuwa Jamus da Faransa kuma ana sa ran Shugaban zai fuskanci matsin lamba daga kasashen game da katse hulda tsakanin Rasha da gwamnatin Bashar al Assad na Syria.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin Reuters
Talla

Putin zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sabon Shugaban Faransa Francois Hollande a ziyararsa ta farko bayan sake zama shugaban Rasha karo na uku.

Putin zai fara kai ziyara ne birnin Barlin kafin ya mika zuwa Birnin Paris. Kuma ziyarar Shugaban na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen Duniya ke matsin lamba ga gwamnatin Bashar al Assad na Syria bayan mutuwar mutane sama da 100 a birnin Huola a karshen mako.

Tuni dai kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya da Amurka da wasu kasashen Yammaci suka katse hulda da Syria bayan kai wani hari da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 108 yawancinsu mata da yara kanana a Houla.

Kafin Ziyarar Putin, Gwamnatin Jamus ta bukaci Rasha daukar matakin katse hulda da Syria.

‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama sun ce akalla mutane 13,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Al Assad a Syria.

A jiya Alhamis ne Sakatariyar Harakokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta soki gwamnatin Rasha akan bijerewa kudirin Majalisar Dinkin Duniya bayan gargadin rikicin Syria na iya rikidewa zuwa yakin basasa.

Wannan ne dai karo na farko da Hollande zai fara ganawa da Putin bayan lashe zaben shugaban kasa a watan jiya.

Mista Hollande yace zai yi kokarin tattaunawa da Putin a ziyararsa zuwa Paris domin ganin Rasha ta yi watsi da kawanceta da Syria.

Rasha da China sun dade suna hawan kujerar na-ki a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game duk wani kudirin daukar mataki akan Syria.

Sai dai ministan harakokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, yace Rasha tana goyon bayan yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Kofi Annan ba gwamnatin Assad ba.

Yanzu haka dai an fara tunanin bin hanyar da aka kawo karshen mulkin Ali Abdullah Saleh na Yemen domin kawo karshen rikicin Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.