Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan tawayen Syria sun ba Gwamnatin Assad sa’oi 48

Bayan kai harin birnin Houla wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 100 a makon jiya, ‘Yan Tawayen Syria, sun ba gwamnatin kasar wa’adin sa’oi 48 domin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta kofi Annan, ko su kaddamar da sabbin hare hare.

Mutane sun taro a lokacin da ake Jana'izar wadanda suka mutu a harin birnin Houla
Mutane sun taro a lokacin da ake Jana'izar wadanda suka mutu a harin birnin Houla REUTERS/Shaam News Network/Handout
Talla

Kanal Qassim Saadeddine, kakakin ‘Yan Tawayen, yace nan da karfe 12 na rana a gobe Juma’a, idan gwamnatin bata fara aiwatar da yarjejeniyar janye dakarunta zuwa bariki ba, zasu yi gaban kansu, wajen fadawa dakarun Assad.

‘Yan tawayen sun bukaci Gwamnatin Assad fara aiki da yarjejeniyar zaman lafiya ta Kofi Annan da ta kunshi tsagaita wuta da kawo karshen zubar da jini da janye muggan makamai a yankunan fararen hula da sakin ‘Yan siyasa da aka kama tare da barin ‘Yan jarida shiga sassan yankunan kasar.

‘Yan Tawayen kuma sun bukaci Gwmanatin kauce wa kai hare hare ga tawagar masu sa Ido ta Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch tace sama da mutane 13,000 ne suka mutu tun fara zanga zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad a watan Maris na shekarar 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.