Isa ga babban shafi
Syria-MDD

MDD ta la’anci kisan kiyashin birnin Huola a Syria

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah Waddai da hare haren da Dakarun Gwamnatin Syria suka kai a birnin Huola, inda mutane 108 suka mutu. Ban Ki-moon ya danganta al’amarin da keta dokokin duniya.

Gawawwakin wadanda aka kashe a birnin Huola a kasar Syria
Gawawwakin wadanda aka kashe a birnin Huola a kasar Syria REUTERS/Shaam News Network
Talla

Hare haren sun yi sanadiyar mutuwar yara kanana 49 da mata 34.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Bashar al Assad ya janye muggan makamai a yankunan da ke da yawan mutane karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta Kofi Annan.

A jiya Lahadi daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga a sassan yankunan Syria domin la’antar kisan kiyashin birnin Huola.

A zauren Majalisar Dinkin Duniya, Birtaniya da Faransa sun gabatar da kudirin la’antar Gwamnatin Assad amma kasar Rasha ta bukaci gudanar da taron gaggawa kafin amincewa da kudirin.

Har yanzu dai gwamnatin Syria ta yi watsi da zarge-zargen kashe kashen da aka daura akan ta.

Sai dai wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu sa ido a Syria sun ce gwamnatin Syria ke da alhakin kai hare haren da ke lakume rayukan fararen hula.

A yau Litinin ne  Kofi Annan zai sake kai ziyara birnin Damascus kuma ana sa ran zai tattauna da Bashar al Assad akan cim ma muradun shi guda shida da suka kulla yarjejeniya da gwamnatin Syria.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 10,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Al Assad a Syria amma ‘yan adawa sun ce mutane 13,000 ne suka rasa ransu a rikicin kasar.

‘Yan adawar sun ce yana da wahala a cim ma bukatun Kofi Annan idan har kasashen duniya basu dauki mataki ba akan gwamnatin Bashar Assad.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.