Isa ga babban shafi
Rasha

An rantsar da Putin matsayin sabon Shugaban Kasar Rasha

Vladimir Putin ya karbi rantsuwar shugabancin kasar Rasha karo na uku bayan an yi taho mu gama tsakanin Jami’an tsaro da masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shi. Putin ya karbi rantsuwar kare ‘Yancin kasar Rasha da mutanenta Bayan ya rungume kundin tsarin mulkin kasar.

'Yan Sandan kasar Rasha suna kokarin cafke wani daga cikin gungun masu zanga-zangar adawa da Putin a jajibirin ratsar da shi a Moscow
'Yan Sandan kasar Rasha suna kokarin cafke wani daga cikin gungun masu zanga-zangar adawa da Putin a jajibirin ratsar da shi a Moscow REUTERS/Mikhail Voskresensky
Talla

Da misalin karfe 8:00 agogon GMT ne aka rantsar da Putin wanda ya gaji shugaba Dmitry Medvedev.

Wannan ne dai karo na Biyar da aka rantsar da wani shugaba a kasar Rasha tun bayan faduwar Soviet.

Sai dai a jajibirin rantsar da Putin an samu mummunan tashin hankali tsakanin Jami’an tsaro da masu zanga zangar adawa da gwamnatin Putin.

‘Yan Sandan kasar, sun kama akalla mutane 400, daga cikin daruruwan masu zanga-zangar adawa da dawowar Gwamnatin Vladimir Putin.

Cikin wadanda aka kama sun hada da shugabanin ‘Yan adawa uku, Alexei Navalny, Boris Nemtsov da Sergei Udaltsov.

Rehotanni daga Rasha na nuni da cewa Jami’an tsaro kimanin 20 sun samu rauni sanadiyar Jifa da duwatsu daga masu zanga-zanga.

Medvedev shi ne shugaban kasar Rasha tun a shekarar 2008 bayan kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa Putin yin tazarce wa’adi na uku a jere.

Mista Putin shi ne shugaban kasar Rasha a shekarar 2000 bayan Boris Yeltsin ya yi murabus.

Sai dai masu sharhi game da Siyasar kasar Rasha suna ganin Putin zai fuskanci kalubale a sabon wa’adin mulkinsa na shekaru Shida saboda wayewar kai da al’ummar Rasha ke samu a Kullum.

Ana sa ran Medvedev zai karbi tsohon mukamin Putin na Fira Minista tare da fuskantar suka saboda rashin cim ma alkawullan da gwamnatinsa ta dauka na ci gaban tattalin arziki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.