Isa ga babban shafi
Rasha-Syria

Taron kawayen Syria cikas ne ga sasanta rikicin kasar, inji Rasha

Gwamnatin kasar Rasha tace taron kasashe masu kiran kansu kawayen Syria da aka gudanar a Istanbul ya sabawa kudirin sasanta kawo karshen jubar da jini da aka kwashe shekara ana yi a Syria.

Fira Ministan kasar Turkiya Tayyip Erdogan a lokacin da yake gabatar da Jawabi a taron kasashe masu kawance da Syria
Fira Ministan kasar Turkiya Tayyip Erdogan a lokacin da yake gabatar da Jawabi a taron kasashe masu kawance da Syria REUTERS/Murad Sezer
Talla

Kasar Rasha ta bayyana damuwa game da matakin tallafawa ‘Yan Tawayen Syria da makamai domin kawo karshen mulkin Bashar Assad.

Kasashen Larabawa sun yi kira ga Shugaban Syria Bashar Assad ya gaggauta cim ma bukatunsu da Koffi Annan ya gabatar domin sansata rikicin kasar.

Shugabannin kasashen sun amince da wakilcin ‘Yan Tawayen Syria a matsayin halatacciyar gwamnatin Syria a taron da suka gudanar a Turkiya.

Majalisar ‘Yan Tawayen Syria tace zata  biya ‘Yan Tawayen da ke yaki da Gwamnatin shugaba Bashar al Assad albashi, da duk wani soja da ya balle daga bangaren Gwamnati.

Kasashen Saudiya da Qatar sun amince da kudirin tallafawa ‘Yan tawayen da Miliyoyin daloli domin ci gaba da yakinsu da Assad.

Amma kasar Iraqi ta yi suka ga matakin kasashen Qatar da Saudiya game da yunkurin tallafawa ‘Yan tawayen Syria.

Kasashen Yammacin Duniya da na Larabawa 70 ne suka halarci taron kawayen Syria da aka gudanar a kasar Turkiya, amma China, Rasha da Iran suka kaurace.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton tace zasu sake tallafawa ‘Yan Tawaye da Karin Dala miliyan 12.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.