Isa ga babban shafi
Sharhin Jaridu

Sharhin Wasu Jaridun Faransa

Kafin gudanar da hutun Ma’aikata da za’a gudanar a gobe Talata, Jaridun Faransa sun mayar da hanakali akan gangamin kungiyoyin kwadago da yakin neman zaben shugaba Nicolas Sarkozy.

Talla

Jaridar La Croix tace Faransawa suna da ‘Yancin gudanar da bukin ma’aikata yadda suka ga dama.

Jaridar tace matsalar rashin aikin yi ita ce babbar matsalar da Faransawa a zamanin nan suke fuskanta amma jaridar tace Sarkozy yana kokarin yin amfani da hutun ma’aikata domin gudanar da yakin neman zaben shi.

Jaridar La Croix tace matsalar rashin aikin yi  ne zata mamaye muhawar kasa da za’a gudanar tsakanin Sarkozy da Hollande.

A Babban labarin Jaridar L'Humanité ta zayyana bukatun Faransawa da suka shafi inganta albashi mai tsoka tare da samun horo wadatacce da ci gaban tattalin arziki da kula da ayyukan bankuna ta la’akari da kudaden hannayen jari.

L'Humanité tace gangamin da ma’aikata zasu hada a gobe zai kasance kalubale ga muhawarar da za’a gudanar tsakanin Sarkozy da Hollande.

A nata bangaren Jaridar Le Figaro ba ta damu da gangamim ma’aikata ba a gobe sai dai ta mayar da hankali ne game da muhawarar da ‘Yan takarar shugaban kasa zasu gudanar a ranar Laraba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.