Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya karyata zargin karbar kudade daga Gaddafi na Libya

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya yi watsi da zargin da ake masa na karbar makudan kudade daga Tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Ghadafi, don gudanar da yakin neman zabensa a shekarar 2007.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yana gaisawa da Marigayi Kanal Gaddafi na Libya
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yana gaisawa da Marigayi Kanal Gaddafi na Libya AP/Francois Mori
Talla

A ranar Assabar ne wani shafin bincike na Mediapart a Intanet ya wallafa wata takarda dauke da tambarin gwamnatin Libya da rubutun Arabiya akan zargin Sarkozy ya karbi makudan kudade a yakin neman zabensa a shekarar 2007.

A bayanin takardar da aka wallafa An zargi Sarkozy da karbar kudade hannun Marigayi Kanal Gaddafi kudi Dala Miliyan Sittin da Shida.

Sai dai Sarkozy yace babu kanshin gaskiya game da zargin da ake ma shi.

Ana ganin labarin da aka wallafa kan iya durkushe kimar shugaban mai fuskantar dimbin matsaloli daga abokin hamayyar shi Francois Hollande.

Kamfanin dillacin Labran Faransa AFP ya tuntubi tsohon jekadan Libya Moussa Koussa wanda kuma ya karyata zargin da ake wa Sarkozy.

A cewar Moussa Koussa takardun na bugi ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.