Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Sharhi game da yadda Hollande zai doke Sarkozy a zagaye na biyu

François Hollande, Dan takarar Jam’iyyar Gurguzu ta socialist shi ne ya samu rinjayen kuri’u a zagaye na farko na zaben shugaban kasa a Faransa, kamar yadda aka yi hasashe kafin gudanar da zaben. A zagaye na biyu akwai has ashen zai iya mamayar kuri’un ‘Yan takarar da suka sha kashi a zagaye na farko Jean-Luc Melenchon Eva Joly.

François Hollande, Dan takarar Shugaban kasa mai hamayya da Sarkozy  karkashin Jam'iyyar gurguzu ta socialist
François Hollande, Dan takarar Shugaban kasa mai hamayya da Sarkozy karkashin Jam'iyyar gurguzu ta socialist AFP/Patrick KOVARIK
Talla

Sai dai yanzu akwai barazana ganin yadda Marine Le Pen ‘Yar Takarar Jam’iyyar National Front ta yi mamaya a zagaye na farko cikin ‘Yan takara 10.

Hollande zai yi fatar magoya bayan Le Pen sun fito zabe tare da fatar ganin sun juya wa Sarkozy baya.

Wadanne hanyoyi ne dan takarar zai bi cikin makwanni biyu domin yakin neman zabensa zagaye na biyu a ranar 6 ga watan Mayu?

Bayan ganawa da Mambobin Jam’iyyarsa a jiya litinin, shugabar Jam’iyyar Socialist Martine Aubry ta shaidawa manema Labarai hanya daya da hollande zai bi ya kai ga nasara:

“ hanya daya ita ce kokarin hada kan Faransawa” inji Aubry

A cewar Aubry zasu fito su shaidawa Faransawa kudirinsu kuma cim ma wannan kudirin yana hannunsu.

Hollande ya bayyana damuwar shi akan nasarar da Le pen ta samu a zagaye na farko. Hollande ya shaidawa manema labarai yanzu lokaci ne da zai saurari magoya bayan Jam’iyyar National Front wadanda suka kadawa Le Pen Kuri’a.

Hollande yace babu wata hanya da zai bude wa Sarkozy ta muhawara kafin zagaye na biyu. Domin a cewar shi amincewa da muhawarar wani mataki ne na karya shirin da suka tsara tun da farko.

Ya zama dole sai magoya bayan Hollande sun fifita yakin neman zabensu a manyan biranen Faransa da suka hada da Paris babban birnin kasar inda aka samu karancin masu kada kuri’a idan har suna neman sake yin mamaya.

Hollande yana neman yin amfani da salon yakin neman zaben Obama a zaben Amurka wajen ganin wadanda suka kauracewa zagaye na farko sun fito kada kuri’a a zagaye na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.