Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy da Hollande zasu fafata a zagaye na biyu na zaben Faransa

Shugaban mai ci Nicolas Sarkozy da dan takarar Jam’iyyar Gurguzu ta Socialist François Hollande, zasu fafata a zagaye na biyu na zaben Faransa bayan Hollande ya samu kashi 28.63, Sarkozy ya smau kashi 27.18 a zagayen farko na zaben shugaban kasa.

François Hollande Dan takarar Jam'iyyar Gurguzu da Nicolas Sarkozy shugaban kasa mai ci
François Hollande Dan takarar Jam'iyyar Gurguzu da Nicolas Sarkozy shugaban kasa mai ci REUTERS/Jacky Naegelen /Eric Feferberg
Talla

A ranar Shida ga watan Mayu ne al’ummar Faransa zasu tantance gari da tsakuwa tsakanin Nicolas Sarkozy da François Hollande.

 

Sai dai wani sakamakon Kuri’un Jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna Francois Hollande, Dan takaran Jam’iyyar Socialists zai kada shugaba Nicolas Sarkozy a zagaye na biyu.

Zaben jin Ra’ayin Jama’ar da  tashar Talabijin ta Faransa da Jaridar Le Monde suka dauki nauyin gudanarwa, ya nuna Hollande zai samu kashi 54 a zagaye na biyu, Sarkozy zai samu kashi 46.

Irin wannan kuri’ar jin ra’ayin jama’a ne Tashar Radiyon Turai ya gudanar wanda ya bada irin wannan sakamako.

Jean Marie Le Pen cikin ‘Yan takara 10 ita ce tazo ta uku da kashi 17.9.

Ana kuma tunanin mai yuwa ne Marie ta goyi bayan Hollande a zagaye na biyu, abinda zai iya bashi damar samun nasara.

Marie tace wannan shi ne somin tabin abinda aka gani, tare da fatan sakamakon zai basu cikakkiyar nasara.

An dai gudanar da zaben ne bisa la’akari da shakkun yadda tattalin arzikin kasar zai kasance, da kuma matsalar yankin kasashe masu amfani da kudin Euro.

Wannan shi ne karon farko da aka samu shugaba mai ci a kasar Faransa yana fuskantar Barazanar iya lashe zabe.

Mahaifin Le Pen ya taba shiga takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2002 kuma ya ba mutane mamaki domin ya samu kashi 16.8 na kuri’u a zagaye na farko a fafatawar shi da tsohon shugaba Jacques Chirac.

Yanzu haka dai wasu ‘yan takara biyu, Eva Joly da Melenchon sun bayyana bada goyon bayansu ga François Hollande a zagaye na biyu domin kayar da Sarkozy.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.