Isa ga babban shafi
Faransa

Chirac yace Hollande zai jefa wa kuri’ar shi a zaben Faransa

Tsohon shugaban kasar Faransa Jacques Chirac yace Francois Holland na Jam’iyyar Gurguzu zai jefa wa kuri’ar shi ba zai zabi dan jam’iyyarsa Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa kamar yadda Jean-Luc Barre abokin tsohon shugaban ya tsegunta.

Jaques Chirac tare da matarsa Bernadette Chirac
Jaques Chirac tare da matarsa Bernadette Chirac REUTERS/Charles Platiau
Talla

Jean-Luc Barre wanda masanin Tarihin Faransa ne yace Chirac ba da wasa ya furta kalaman shi ba kamar yadda ya shaidawa Jaridar Le Parisien.

Sai dai ofishin Chirac ya musanta labarin domin Mamban Jam’iyyar UMP ne mai mulkin Faransa.

Chirac wanda ya shugabanci Faransa tsakanin shekarar 1995 zuwa 2007, a bara ya fito fili ya bayyana kudirinsa na zaben Hollande maimakon Sarkozy.

Jaridar Le Parisien tace akwai sabanin ra’ayi da aka samu tsakanin iyalan Chirac domin Matarsa Bernadette tace Sarkozy zata ba kuri’arta.

A ranar Lahadi ne al’ummar Faransa zasu kada kuri’a a zaben zagaye na farko kafin shiga zagaye na biyu a ranar 6 ga watan Mayu. Amma zaben Jin ra’ayin Jama’a da aka gudanar ya nuna Hollande ne zai lashe zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.