Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy da Hollande sun hada gangamin magoya baya a Paris

‘Yan Takaran shugabancin Faransa guda biyu, Shugaba Nicolas Sarkozy, da Francois Hollande na Jam’iyyar Gurguzu, sun samu halartar dubban magoya baya, a yakin neman zabensu a birnin Paris, inda ya rage saura kwanaki a gudanar da zabe zagaye na farko a ranar 22 ga watan Afrilu.

Gangamin Taron yakin neman Zaben  Nicolas Sarkozy da Gangamin taron François Hollande a zaben shugaban kasar Faransa da za'a gudanar a bana
Gangamin Taron yakin neman Zaben Nicolas Sarkozy da Gangamin taron François Hollande a zaben shugaban kasar Faransa da za'a gudanar a bana © Reuters
Talla

Tarukan gangamin na ‘Yan takarar da aka gudanar a jiya lahadi a birnin Paris, ya nuna al’ummar kasar Faransa sun rabu biyu.

Sarkozy ya gudanar da taron yakin neman zabensa ne a dandalin Concorde, hollande kuma ya hada gangamin masoya a Vincennes da ke gabacin birnin Paris.

Tuni dai sakamakon zaben jin ra’ayin jama’a ya nuna ‘yan takarar guda biyu ne zasu yi mamaya tsakanin ‘Yan takara 10 masu neman kujerar shugabancin kasar.

Wani sakamakon zaben ra’ayin Jama’a da aka gudanar a baya bayan nan ya nuna Sarkozy zai samu yawan kuri’u a zagaye na farko amma Shugaban zai sha kaye a zagaye na biyu na zaben da za’a gudanar a 6 ga watan Mayu.

A yakin neman zabensa Sarkozy ya bukaci magoya bayansa kada su ji fargabar komi wadanda yawancinsu masu Manyan shekaru ne.

A dandalin Concorde ne Charles de Gaulle da Jacques Chirac tsoffin shugabannin kasar suka gudanar da gangamin zabensu, kuma Sarkozy ya yi amfani da wannan damar ne domin cim ma nasarar da ya samu a zaben shekarar 2007.

Sai dai a gangamin Hollande, magoya bayansa su yi ta shewar la’antar shirin Sarkozy na yaki da bakin haure.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.