Isa ga babban shafi
Faransa

Zaben Faransa: Sharhin Jaridu a Yau

Yanzu haka Jaridun kasar Faransa sun fara sharhi game da zaben shugaban kasa da za’a gudanar, kuma Jaridar Liberation ta ruwaito wasu tambayoyi Biyar da zasu zama kalubale ga 'Yan takara da kuma shi kan shi  zaben Shugaban kasar..

Talla

Da farko Jaridar ta fara tambayar mutane nawa ne zasu fito zaben domin kada kuri’a?
A zabukan da suka gabata mutane da dama a kasar sukan kauracewa zabe domin idan aka samu kashi 20 na masu kada kuri’a mataki ne da Jam’iyyun siyasa ke nuna farin cikinsu.

Ta haka ne ‘Yar Takarar Jam’iyyar National Front, Jean Marie Le Pen ta samu rinjaye kuri’u fiye da dan takarar Jam’iyyar socialist Lionel Jospin a zaban shekarar 2002.

Wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna cewa kashi 32 na masu kada kuri’a zasu kauracewa zaben shugaban kasar da za’a gudanar a bana.

Tambayar Jaridar Liberation ta biyu, ita ce, Ko wane dan takara ne zai lashe zaben a zagaye na farko? Jaridar dai ta yi la'akari ne da Manyan ‘yan takara a zaben, François Hollande na jam’iyyar gurguzu da Nicolas Sarkozy wadanda dukkaninsu suna gogayya da juna a zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar game da wanda zai iya lashe zaben a zagaye na farko.

Shugaba Sarkozy yace yana bukatar lashe zaben shugaban kasa zagaye na farko, domin yana ganin idan ya samu nasarar zuwa na farko a zagayen farko, zai samu damar kaddamar da sabon yakin neman zaben shi a zagaye na biyu.

Sai dai Jaridar Le Figaro ta ruwaito labarai masu dadi da akasin haka ga Sarkozy, domin jaridar tace Sarkozy zai iya lashe zabe idan aka yi la’akari da manufofin shi na inganta tsaro a da yaki da bakin haure da kuma kare manufofin Faransa. Amma jaridar tace Hollande zai iya lashe zaben ta yin amfani da manufofin shi game da ci gaban Ilimi da kyautata rayuwar Faransawa.

Idan muka dawo ga tambayar Liberation ta uku, Jaridar ta nuna fargaba ne game da masu goyon bayan François Bayrou wadanda ta yi hasashen zasu iya marawa Sarkozy baya saboda yadda dan takararsu ke nuna adawa da Jam’iyyar Socialist. Kodayake ba lalle bane ya marawa Sarkozy baya.

Sannan wani abin la’akari a zaben Faransa shi ne game da rawar da ‘yan takara guda biyu zasu taka masu tsatsstauran ra’ayi; Marine Le Pen da kuma Jean-Luc Mélenchon

Jaridar Liberation daga karshe tace François Hollande zai fi samun magoya baya a zagaye na biyu fiye da Sarkozy. Amma idan magoya bayan Le Pen da Bayron suka dawo bayan Sarkozy, Sakamakon zaben zai iya ba Nicolas Sarkozy nasara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.