Isa ga babban shafi
Faransa

Segolene ta bada goyon bayanta ga Hollande a zaben Faransa

Tsohuwar ‘Yar Takarar shugabancin kasar Faransa, Segolene Royal, ta bayyana bada goyan bayanta ga Francois Hollande, wanda ake ganin zai iya kada shugaba Nicolas Sarkozy a zabe mai zuwa.

A lokacin da  Ségolène Royal ke bada goyan bayanta ga o François Hollande, a birnin Rennes, domin kalubalantar Sarkozy a zaben Faransa
A lokacin da Ségolène Royal ke bada goyan bayanta ga o François Hollande, a birnin Rennes, domin kalubalantar Sarkozy a zaben Faransa Reuters
Talla

Yakin neman zaben Francois Hollande ya samu ci gaba a birnin Rennes, lokacin da Segolene Royal, wacce ta fafata da shugaba Nicolas Sarkozy a zaben shekarar 2007, ta bayana goyan bayan ta ga takarar shi.

Masu nazarin siyasar Faransa na kallon wannan goyan baya a matsayin gagarumin ci gaba, da kuma dinke barakar da ke tsakanin mutanen biyu, wadanda a da, suka zauna tare, kuma suka haifi yara biyu, ba tare da aure ba.

Rahotanni sun ce, mutane kusan 18,000 suka halarci taron gangamin, wanda yake dada jaddada yadda Hollande ke kara tagomashi, yayin da zaben ke kara karatowa.

Hollande ya bayyana manufofin sa da suka hada da rage hauhawan farashin mai, rage albashin jami’an Gwamnati da kashi 30, da kuma bada tallafi ga iyalai.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.