Isa ga babban shafi
Faransa

Idan Moody ya rage darajar Faransa laifin Sarkozy ne, inji Hollande

Dan Takarar shugabancin kasar Faransa, Francois Hollande, ya shaidawa Rediyo Faransa cewa idan kamfanin da ke rage darajar cin bashi na Moody ya rage darajar kasar Faransa bayan zaben watan Mayu, zai kasance laifin shugaba Nicolas Sarkozy idan har ya gaji gwamnatinsa.

François Hollande Dan takarar Jam'iyyar Gurguzu a zaben shugaban kasar Faransa
François Hollande Dan takarar Jam'iyyar Gurguzu a zaben shugaban kasar Faransa RFI
Talla

Hollande wanda shi ne babban mai hamayya da Sarkozy a zaben shugaban kasa yace kamfanin Moody yana amfani ne da bayanan da ya tattara, kuma Kamfanin ya yi gargadin zai rage darajar biyan bashin kasar Faransa.

A cewar Hollande, duk wani mataki da zai fito bayan zaben shugaban kasa, zai zama abinda gwamnati mai barin gado ne ta yi.

Mako daya ne ya rage a jefa kuri’ar zaben shugaban kasa zagaye na farko a Faransa kuma Hollande yace zai inganta tattalin arzikin kasar idan ya lashe zabe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.