Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyyar Sarkozy ta yi tir da tsoffin Ministocinta a Faransa

Jam’iyyar UMP ta shugaba Nicolas Sarkozy, ta soki wasu Tsoffin ministocinta, wadanda suka bayyana ba zasu zabi Shugaban ba a zabe mai zuwa bayan bayyana kudirin nuna goyan bayansu ga Dan takarar adawa Francois Hollande.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy Dan takarar Shugaban kasa karkashin Tutar Jam'iyyar UMP
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy Dan takarar Shugaban kasa karkashin Tutar Jam'iyyar UMP REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Jam’iyar ta bayyana ministoci a matsayin maciya amana, wadanda bai kamata a sake amincewa da su ba.

Shugaba Sarkozy yanzu haka yana fuskantar kalubale game da zabensa wa’adi na biyu a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a karshen mako, domin mutane da dama suna kaurace masa, cikinsu har da ‘yayan Jam’iyarsa, da kuma Tsohon shugaban kasar da ya gada, Jacques Chirac.

Sakamakon ra’ayoyan Jama’a da aka gudanar a kasar sun nuna Sarkozy zai sha kaye a zaben, kodayake sakamakon ya nuna shugaban zai iya lashe zagaye na farko amma Hollande babban mai adawa da shi na Jam’iyyar gurguzu shi zai lashe zagaye na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.