Isa ga babban shafi
Faransa

Sharhin Jaridun Faransa

Sakamakon zaben Faransa ne ya mamaye kanun labaran Jaridun kasar bayan kammala zagaye na farko inda sakamakon zaben yaba François Hollande nasara akan Shugaba Nicolas Sarkozy. ‘Yar takara Marine Le Pen ta Jam’iyyar National Front ta samu nasarar zuwa a matsayi na Uku.

Wasu Jaridun kasar Faransa
Wasu Jaridun kasar Faransa
Talla

Le Pen ta samu yawan kuri’u kashi 18 fiye da mahaifinta wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2002 nasarar da tasa ya kai shiga zagaye na biyu.

Labarin nasarar Le pen ce ya ja hankalin Jaridun Faransa, domin kimanin mutane Miliyan Bakwai ne suka jefa mata Kuri’a.

Jaridar Business Daily ta danganata Nasarar Le pen a matsayin “girgizan kasa” Amma Jaridar liberation ta danganta nasarar a matsayin “Abun Damuwa”.

Jaridar Le Figaro kuma ta danganta nasarar Le Pen akan ci gaban Jam’iyyarta da kuma yakin neman zabenta wajen magance matsalar tattalin arziki.

A cewar Jaridar Le Figaro, yanzu dole Sarkozy sai ya nemi hanyoyin da zai jawo hanaklin magoya bayan Le Pen domin kada masa kuri’a.

Jaridar tace akwai yiyuwar Sarkozy ya samu daidaito tsakanin shi da Jam’iyyar Le Pen saboda zaben ‘Yan Majalisu da za’a gudanar anan gaba don samun rinjaye.

A daya bangaren kuma dole sai Sarkozy ya nemi Faransawan da suka kada kuri’arsu ga François Bayrou.

Dangane da zaben Jin ra’ayin Jama’a kafin zaben Zagaye na Farko, Jairdar Le Monde tace zaben jin ra’ayin Jama’a 375 aka gudanar kuma Jaridar ta yi hasashen akwai wasu 25 da za’a gudanar a nan gaba.

A cewar Jaridar, Sakamakon zaben zagaye na farko ya sabawa sakamakon zaben jin ra’ayin Jama’a, domin Le Pen ta bada mamaki amma Melechon ya sha kashi, kodayake jaridar tace Bayrou ya samu kuri’un da aka yi hasashen zai samu.

Wani sakamakon Zaben Jin ra’ayi da aka fitar bayan kammala zagaye na farko, an bayyana François Hollande zai lashe zagaye na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.