Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Sharhi game da yadda Sarkozy zai doke Hollande a zagaye na biyu

A Tarihin zaben shugaban kasa a Faransa, Nicolas Sarkozy shi ne shugaba na Farko da ya sha kaye a zagayen farko, amma duk da haka shugaban yana da kwarin gwiwar lashe zabe a duk lokacin da ya fito yana jawabi a gaban Faransawa.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy kuma dan takarar shugaban kasa karkashin tutar Jam'iyyar UMP a lokacin da yake yakin neman zabensa a gaban Faransawa
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy kuma dan takarar shugaban kasa karkashin tutar Jam'iyyar UMP a lokacin da yake yakin neman zabensa a gaban Faransawa REUTERS/Yves Herman
Talla

A zagayen farko na zaben Faransa, Sarkozy bai sha da dadi ba, domin hasashen da aka yi kafin zaben shi ne ya tabbata.

Dan takarar Jam’iyyar gurguzu ta socialist, François Hollande shi ne ya samu rinjayen kuri’u da kashi biyu fiye da Sarkozy, akwai kuma barazana da Sarkozy ke fuskanta daga ‘Yar takarar National Front Marine Le Pen domin ta samu kashi 18.06 a zagayen Farko.

Masu sharhin siyasa sun yi hasashen yana da wahala Le Pen ta shawarci magoya bayanta domin kadawa Sarkozy kuri’a. Masana dai suna ganin Le Pen zata jagoranci yakin kayar da Sarkozy domin karya Jam’iyar shi ta UMP.

Le Pen tace a ranar 1 ga watan Mayu ne zata yi jawabi game da matsayinta. Amma yana da wahala idan ta bayyana goyon bayanta tsakanin Sarkozy da Hollande, wasu magoya bayanta su bayar da Kuri’arsu ga 'Yan Takarar biyu.

Ya zama dola sai Sarkozy ya nemi kuri’un magoya bayan François Bayrou kashi 9.11 da suka zabe shi a zagayen farko. Tare da neman Kuri’un magoya bayan Marine Le Pen.

Masu fashin baki siyasar Faransa suna ganin yakin neman zaben sarkozy kafin zagaye na biyu yana da jan aiki a gaban shi wajen neman goyon bayan Le Pen da Bayrou.

Wani sakamakon Zaben da kamfanin Ipsos ya fitar ya nuna cewa akwai sabani tsakanin manufofin Le Pen da manufofin Sarkozy game da inganta batun bin doka da Oda da karfafa tattalin arziki da kuma manufofinsu akan shige da fice.

Don haka masu sharhi suna ganin akwai yiyuwar magoya bayan Le Pen zasu juya wa Sarkozy baya a zagaye na biyu.

Akan haka ne kuma Sarkozy ke neman gudanar da muhawara sau uku domin kalubalantar abokin karawar shi François Hollande maimakon Muhawara daya da ake shiryawa kafin shiga zagaye na biyu.

Salon Sarkozy shi ne gabatar da Jawabi tare da mika sakon shi ga daukacin al’ummar Faransawa. Domin shugaban ya yi zargin kafofin yada labaran Faransa wajen nuna goyon bayansu ga ‘Yan adawa.

Sai dai Hollande yace zai kauracewa duk wata Muhawara sabanin muhawara ta kasa da za’a gudanar.

Amma Sarkozy yana ganin Muhawara daya ba zai isa al’ummar Faransa su fahimci matsalolin Faransa ba wadanda Hollande yace zai yi maganinsu baki daya.

Yawancin Magoya bayan Sarkozy a zaben shekarar 2007 sun fice daga Jam’iyyarsa ne zuwa Jam’iyyar Natonal Front ta Merine Le Pen saboda tsatstsauran ra’ayin shi akan tsarin shige da fice.

Don haka akwai babban kalubale a gaban Sarkozy wajen neman amincewar magoya bayan Le Pen.

Magoya bayan Sarkozy suna kokarin ganin an gudanar da muhawara game da tsarin shige da fice domin fahimtar Matsayin Sarkozy akan Matsayinsa ga batun bakin haure.

A yakin neman zabensa zagaye na biyu sai Sarkozy ya yi kokarin nuna wa Faransawa irin rawar da ya taka wajen magance matsalar tattalin arzikin kasashen Turai tare da bayyana fatan shi wajen inganta tattalin arzikin Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.