Isa ga babban shafi
Faransa

Zaben Faransa: Hollande da Sarkozy sun fara sukar Juna kafin muhawara

A ranar 2 ga watan Mayu ne za’a gudanar da Muharawa tsakanin Nicolas Sarkozy da François Hollande kafin zaben shugaban kasa zagaye na biyu, amma ‘Yan takarar guda biyu sun fara Sukar Juna. Hollande ya soki Sarkozy a matsayin makaryaci

Nicolas Sarkozy da François Hollande wadanda zasu fafata a zagaye na biyu na zaben Faransa na shekarar 2012
Nicolas Sarkozy da François Hollande wadanda zasu fafata a zagaye na biyu na zaben Faransa na shekarar 2012 Reuters/Montage Anthony Terrade
Talla

Dambarwar Siyasa dai ta fara kunno kai a Faransa bayan da Shugaba mai Ci Nicolas Sarkozy ya fito a kafar Telebijin yana shaidawa Faransa wani shaihin Malamin kasar Switzerland Tariq Ramadan yana goyon bayan takarar Hollande. A Cewar Sarkozy Malam Ramadan ya fito a gidan rediyo yana kiran a zabi Hollande.

Yanzu haka dai Hollande da Ramadan sun karyata kalaman Sarkozy.

Sarkozy yana neman sabunta hanyoyin yakin neman zabensa domin jawo hankalin mutane Miliyan Shida magoya bayan Marine Le Pen ‘Yar takarar da tazo na uku a zagayen farko.

Yakin neman zaben Sarkozy shi ne rage kwararar baki a Faransa tare tsaurara matakan shige da fice a kasar, al’amarin da yasa daruruwan magoya bayan Jam’iyyarsa suka juya zuwa ga Jam’iyyar National Front ta Marine Le Pen.

Sarkozy ya musanta rehotanni da suka ce ba zai ba Jam’iyyar Le Pen mukaman Minista ba a gwamnatinsa idan ya kai ga nasara.

Kafar Telebijin ta Faransa zata gudanar da muhawara tsakanin ‘yan takarar guda biyu.

Ana hasashen Sarkozy zai yi kokarin kalubalantar abokin hamayyar shi game da batun shige da fice da Haraji da alkawalin Hollande na daukar Malaman makaranta 60,000.

A Muhawar da za’a gudanar, Sarkozy da Hollande zasu yi kokarin ganin sun gamsar da magoya bayan Le Pen domin samun kuri’arsu.

Amma Marine Le Pen ta yi kiran ‘Yan Takarar guda biyu su dai na tallar hajarsu ga magoya bayanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.