Isa ga babban shafi

An kama mutane 15 da ke kokarin kutse a sakamakon zaben jihar Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina na gudanar da bincike kan wasu mutane 15 da ake zargi da laifin yin kutse a harakokin zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisa.

Wani dan sandan Najeriya, tare da jami'in hukumar zaben kasar INEC yayin daukar kayan aikin zabe daga ofishin hukumar ta INEC da ke garin Yola a Adamawa zuwa wasu sassan jihar. 15/02/2019.
Wani dan sandan Najeriya, tare da jami'in hukumar zaben kasar INEC yayin daukar kayan aikin zabe daga ofishin hukumar ta INEC da ke garin Yola a Adamawa zuwa wasu sassan jihar. 15/02/2019. REUTERS/Nyancho NwaNri
Talla

Yayin da ‘yan Najeriya ke zaben sabon shugaban kasa da wakilansu a majalisar dokokin kasar,Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isa, wanda ya yi wa manema labarai karin haske a yammacin jiya Juma’a, ya ce an kama wadanda ake zargin da na’urorin lantarki da dama da suka hada da na’urori masu kwakwalwa.

'Yan sanda suna gudanar da bincike kuma za a bayyana sakamakon ga jama’a a cewar SP Gambo Isa.

Jami’in ya bayyana cewa sun gayyaci masana da nufin tantance ainihin manufar wadanan mutane da ‘yan Sanda suka kama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.