Isa ga babban shafi
Kasuwanci

Kasuwar Mile 12 dake Legas ta kayyade farashi saboda watan Ramadana

Wallafawa ranar:

Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida da hankali ne kan yadda farashin kayan masarufi ke hauhawa a lokacin azumin watan Ramadana a kowace shekara musamman a manyan biranen Najeriya. A mafiya yawan lokuta farashin kayayyakin masarufi, kayan abinci da na sha, na fuskantar tashin gwauron zabo bisa la’akari da bukatun kayan don yin amfani da su a lokacin azumi.

Wani sashe na ’yan tumatir da ke kasuwar Mile 12
Wani sashe na ’yan tumatir da ke kasuwar Mile 12 Aminiya
Talla

Sai dai kasuwar Mile 12 International dake birin Legas a Najeriyar wadda ke zama daya daga cikin kasuwannin kayan gwari da na abinci mafi girma a Afirka ta kayyade farashin saboda azumin, ko da yake masu saye da sayarwa na kokawa da tsadar kayyaki da shugabannin kasuwar ke cewa, idan ba don matakin da suka dauka ba to da lamarin zai zarta haka.

Mile 12 international market in Lagos --Nigeria
Mile 12 international market in Lagos --Nigeria © RFI Hausa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.