'Yan kasuwar Mile 12 sun danganta hauhawan farashi da rashin tsaron Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:49
Shirin Kasuwa 'Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida da hankali ne kan tsadar rayuwa da hauhawan farashin kayyaki da ake fuskata a Najeriya masamman a birnin Lagos dake kudu maso Yammacin Kasar.
Yayin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan tsadar rayuwa saboda hauhawan farashin kayayyaki da akasari ake daura alhaki kan yakin Rasha da Ukraine, wasu 'yan kasar na diga ayar tambaya kan ko me ya kawo tsadar kayayyaki da ake samarwa a cikin gida masamman ma na bangaren amfanin gona.
Kasuwar kayan gwari mafi girma a Afirka
Wannan ya sa shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' ya kai ziyara kasuwar Mile 12 international dake birnin Lagos a kudancin Najeriya daya daga cikin kasuwannin kayan abinci mafi girma a nahiyar Afirka masamman ta fannin kayan gwari irinsu tumatur, barkwano, albasa da kayan marmari da dai sauransu...
Kafin mu shiga cikin kasuwar sosai sai da muka leka ofishin shugaban kasuwar ta Mile 12 Alhaji Shehu Usman Jibrin Sanfan, wanda ya fara bayani kan girman kasuwar da yadda takai ake kiranta da kasuwar Duniya.
Matsalolin tsaron sun haifar da hauhawan farashi
Akasarin wadanda muka tattauna da su ciki harda shugaban kasuwar Alhaji Shehu sun dora alhakin tsadar rayuwa da hauhawan farashin kayayyakin kan halin matsalolin tsaro da Najeriyar ke fuskanta yanzu haka.....
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu