Isa ga babban shafi
Kasuwanci

Yadda gobara ta kone kasuwar Monday Market da ke jahar Borno a Arewacin Najeriya

Wallafawa ranar:

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" ya maida hankali ne kan iftila’in da ya afkawa jahar Borno da ke arewacin Najeriya wato konewar babbar kasuwar Maiduguri da akafi sani da Monday Maket.Gobarar da ba’a kai ga sanin musabbabinta har yanzu, ta lakume shaguna da dama a kasuwar mafi girma a yankin arewa maso gabashin Najeriya.Gwamnan jahar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da yayiwa al’ummar jihar jawabi jim kadan bayan afkuwar lamarin, ya kuma yi kira da akauce alkanta iftila’in da siyasa.

Jami'an kwana-kwana a kasuwar Monday Market
Jami'an kwana-kwana a kasuwar Monday Market © rfi hausa
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.