Siyasa na kokarin haddasa rarrabuwar kai tsakanin jaruman Kannywood
Wallafawa ranar:
Kunna - 20:00
Shirin dandalin nishadi tare da Salissou Hamissou da taimakon Hauwa Kabir, ya mayar da hankali kan yadda can a masana'antar Kannywood siyasa ke shirin haddasa gagarumar matsala bayan samun rarrabuwar kai tsakanin jarumai bayan zaben gwamnonin da ya gudana a Sassan Najeriya
Can a Jamhuriyyar Nijar kuma, shirin a wannan mako ya tattauna da matashin mawaki Safiyanu Super Star wanda tauraruwarsa ke ci gaba da haska bayan farfadowa daga koma bayan da ya fuskanta.
Haka zalika akwai yadda ta ke kayawa a bukukuwan gasar kalankuwar fina-finan mata can a kasar Faransa.
Ku latsa alamar sauti don saurarin cikakken shirin......
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu