Amb Ibrahim Kazaure kan janye takunkumin ECOWAS ga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:31
Kungiyar ECOWAS ta sanar da janye takunkumin karya tattalin arzikin da ta sanyawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, yayin da ta bukaci sojojin da suka yi juyin mulki a wadannan kasashe da su dawo teburin tattaunawa domin samo hanyar mayar da mulkin dimukiradiya a cikin su. Shugabannin ECOWAS sun ce an cire takunkumin ne saboda dalilan jinkai, kuma matakin ya kawo karshen hana zirga zirgar jiragen sama da bude asusun ajiyar wadannan kasashe guda 3.
Dangane da tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, masanin harkar diflomasiya.
Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana.....
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu