Isa ga babban shafi

CEDEAO ta dage takunkuman da aka kakabawa Nijar

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a taron da ya gudana a yau Asabar a Abuja sun yanke shawarar dage wani kaso mai yawa na takunkumin da aka kakabawa Nijar.

 Bola Tinubu Shugaban kungiyar ECOWAS a Abuja
Bola Tinubu Shugaban kungiyar ECOWAS a Abuja AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Shugaban kungiyar ta ECOWAS Omar Alieu Touray ya sanar cewa ECOWAS "ta yanke shawarar dage takunkumi mafi girma da aka kakabawa Nijar tun bayan juyin mulki da ya yi awon gaba da shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli 2023.

Omar Alieu Touray ya ce za a sake bude iyakokin Nijar da sararin samaniya, za a sake ba da izinin hada-hadar kudi tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar, da kuma baiwa jama’a damar kai da kawo kamar dai yada aka saba gani a baya.

Ya kuma bukaci "a gaggauta sakin" hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum, wanda gwamnatin soja ta tsare shi da matarsa ​​tsawon watanni bakwai.

Taron kasashen ECOWAS a Abuja
Taron kasashen ECOWAS a Abuja AFP - KOLA SULAIMON

Mali, Burkina Faso da Guinea, da kuma gwamnatocin sojoji na karkashin  takunkumin ECOWAS.

"Dole ne mu sake duba tsarin mu na dawo da tsarin mulki a cikin kasashe hudu na mu," in ji a gabatarwar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ke rike da shugabancin ECOWAS, dangane da Mali, Burkina Faso, Nijar da Guinea.

Masu adawada manufofin ECOWAS
Masu adawada manufofin ECOWAS REUTERS - STRINGER

Wadannan takunkuman sun ciwa kasar ta Nijar da ke yankin Sahel tuwo a kwarya, inda matsanancin talauci ya zarta kashi 40 bisa dari a cewar bankin duniya.

Taron Shugabanin kasashen ECOWAS a Abuja
Taron Shugabanin kasashen ECOWAS a Abuja © KOLA SULAIMON / AFP

Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, wadanda musamman suka juya wa Faransa baya, kuma suka matsa kusa da Rasha, sun hade a cikin kawancen kasashen Sahel (AES).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.