Benin ta dakatar da kwashe kaya daga tashar jiragen ruwan Cotonou zuwa Nijar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:38
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta ce ba za ta bari a kwashe kayayyakin da aka sauke a tashar jiragen ruwan Cotonou zuwa Nijar ba, amma a maimakon haka za ta bai wa ‘yan kasuwar Nijar damar karkata akalar kayayyakin zuwa wasu kasashe, ta hanyoyin mota ko jiragen ruwa.
A sanarwar da ta fitar karshen mako, hukumar kula da tashar jijagen ruwan Cotonou ta kuma bai wa ‘yan kasuwar Nijar damar sayar da kayayyakinsu a Benin idan har ba za su karkata akalarsu zuwa wata kasa ba.
Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Yacouba Dan Maradi, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da ke shigar da kaya a Nijar, domin jin yadda suke kallon wannan mataki. Ga kuma zantawarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu