An fara taron zaman lafiya da tsaro na kasashen Afirka karo na 7 a Dakar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:52
A ranar Litinin aka bude taron zaman lafiya da tsaro karo na 7 a Dakar, babban birnin kasar Senegal wanda zai maida da hankali kan tasirin cutar Korona a fadin nahiyar da kuma matsalolin tsaron yanar gizo, ta'addanci, da kuma sauyin yanayi.
An kafa dandalin zaman lafiyar da tsaro na Dakar dake gudana a duk shekara ne yayin taron Faransa da Afirka da aka yi a birnin Paris a shekara ta 2013, kuma a cikin shekarun da suka shige, ya zama fage ga masu yanke shawara a Afirka.
Kan wannan taro ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Yahuza Getso masanin tsaro dake Tarayyar Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu