Isa ga babban shafi

Jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar

Jakadar Faransa a Jamhuriyar Nijar Sylvain Itte, ya fice daga kasar a safiyar yau Laraba, duk da cewar akwai mutum guda da aka bari a matsayin wakilin Faransa a kasar, kamar yadda wasu majiyoyi tsaro suka tabbatar.

Ofishin jakadancin Faransa da ke Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Ofishin jakadancin Faransa da ke Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar. AFP - -
Talla

A karshen watan da ya gabata ne, sojojin da suka yi juyin mulkin na Nijar suka bai wa jakadan na Faransa sa’oi 48 ya fice daga kasar.

Da farko Faransa ta ki amincewa da umarnin, sabida yadda ba ta amince da sahihancin gwamnatin sojin da ta gudanar da juyin mulkin, lamarin da kuma ya haddasa zanga-zanga a ofishin jakadancin Faransa da ke Nijar.

A wannan watan ne kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana cewar hukumomin mulkin sojin Nijar sun yi garkuwa da jakada Itte da ma’aikatansa a ofishin jakadancinsu.

Amma kuma a karshen makon da ya gabata, shugaba Macron ya bayyana cewar za su janye jakadansu da kuma kwashe sojojinsu kimanin dubu daya da dari biyar da ke Nijar.

Alaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu ne, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Muhammad Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.