Isa ga babban shafi

Sojojin Faransa sun shiga tattaunawa da sojin Nijar kan ficewarsu

Sojojin Faransa na tattaunawa da takwarorinsu a Nijar game da saukaka yadda za a janye sojojin Faransa da kayayyakin aikinsu, kamar shugabannin juyin mulki suka bukaci a yi. 

Sojojin Faransa a Nijar.
Sojojin Faransa a Nijar. © AP/Jerome Delay
Talla

Majiyar Ma'aikatar Tsaron Faransa ta shaida wa Kamfanin Dilancin Labarai na AFP cewa, an fara tattaunawa kan yadda za a fara janye wani adadi na dakarun Faransa da ke kasar, ba tare da wani cikakken bayani kan adadin ko lokaci ba.  

Tun farko makusanta ga ministan tsaron Faransa Sebastien Lecornu sun tabbatar wa AFP cewar, sojojin Faransa na tattaunawa da takwarorinsu na Nijar kan tsarin daidaita aiki tsakaninsu da kuma zirga-zirga na yau da kullum. 

Kafin wannan sanarwa, sabon firaministan Nijar da sojoji suka nada Ali Mahaman Lamine Zeine ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntubar juna game da yadda sojojin Paris za su janye daga kasar cikin gaggawa. 

Faransa na da sojojin kimanin 1,500 da ta jibge a Nijar a wani bangare na ayyukan yaki da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel. 

Sai dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Nijar da Faransa, wacce ta yi mata mulkin mallaka, bayan da Paris ta tsaya tsayin-daka wajen goyon bayan hambarerren shugaban kasar Mohamed Bazoum da sojojin suka yi wa  juyin mulkin a watan Yuni. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.