Isa ga babban shafi

Jakada Sylvain Itte ya isa Faransa bayan barin Nijar a safiyar yau

Jakadan Faransa a Nijar Sylvain Itte ya isa gida Paris da tsakar ranar yau laraba, bayan baro kasar ta yankin yammacin Afrika da asubahin yau biyo bayan dambarwar kasashen biyu game da bukatar ficewarsa sakamakon juyin mulkin soji da ya kawar da halastaciyar gwamnatin demokradiyya.

Ginin Ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai na Nijar.
Ginin Ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai na Nijar. AFP - -
Talla

Da asubahin yau Laraba ne Sylvain Itte ya fice daga birnin Yamai inda jirginsa ya nufi Chadi gabanin tunkarar gida Paris, lamarin da ya kawo karshen takaddamar bukatar ficewar shi daga kasar wadda ta koma karkashin mulkin Soji.

Tsawon makwanni aka shafe ana takun saka kan ficewar jakadan, tun bayan da Sojojin da ke mulki a kasar suka mika bukatar ficewar ta shi a karshen watan Agustan da ya gabata inda suka bashi wa'adin sa'o'i 48, amma kuma Faransa ta kekasa kasa tare da kafa hujjar jakadan ya je kasar ne karkashin halastacciyar gwamnatin Demokradiyya kuma sai a irinta ne zai bar Nijar, lamarin da ya haddasa mabanbantan zanga-zangar bukatar ficewar jakadan.

Yayin wani jawabi da shugaba Emmanuel Macron ya gabatar a ranar Lahadin da ta gabata ne ya sanar da shirin janye jakadan dama dukkanin jami’an Diflomasiyyar Paris a Yamai baya ga ilahirin Sojojin kasar da ke taimakawa wajen yaki da ta’addanci a lokacin mulkin demokradiyyar Nijar.

Kafin wannan mataki dai shugaba Macron ya zargi Sojin na Nijar da garkuwa da jakadan bayan da suka killace shi tare da janye duk wata kariyar diflomasiyyar da ya ke da ita.

Har zuwa yanzu dai Faransa ba ta amince da halascin gwamnatin Sojin ta Nijar ba, batun da ke ci gaba da dagula alakar kasashen biyu da ke matsayin abokai a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.