A yanzu dai ta tabbata cewa Faransa za ta janye jakada da kuma dakarunta dubu daya da 500 daga ?Jamhuriyar Nijar, bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokuradiyya da kuma zanga-zangar adawa da Faransa da aka share tsawon makwanni ana yi a kasar ta Nijar.
To sai dai a zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, kwararren jami’in diflomasiyya kuma tsohon jakadan Najeriya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ambasada Alhaji Abubakar Chika, ya ce babban abin takaici ne yadda alaka ta yi tsami a tsakanin kasashen biyu masu dogon tarihi.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu