Isa ga babban shafi

ECOWAS na tattauna yadda za ta tura sojojinta zuwa Nijar

Manyan hafsoshin sojojin kasashen yammacin Afirka za su gana a cikin kwanaki masu zuwa domin game da shirye-shiryen yiyuwar amfani da karfin soji a Nijar, kamar yadda kakakin kungiyar kasashen yankin ya bayyana a ranar Juma'a, yayin da ake kara nuna damuwa kan halin da ake ciki na tsare hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai © REUTERS/Balima Boureima/File Photo
Talla

Kungiyar ECOWAS ta ba da umarnin a fara aikin soji a ranar Alhamis, makwanni biyu bayan hambarar da gwamnatin Bazoum a juyin mulki karo na bakwai da aka yi a yammaci da tsakiyar Afirka cikin shekaru uku.

Taron shugabannin hafsoshin ya yi nuni da cewa, kasashen yammacin Afirka na kara daukar matakan da suka dace domin ganin an kawo karshen juyin mulkin.

Wani jami'in Najeriya da majiyar sojojin Ivory Coast sun ce za a gudanar da taron ne ranar Asabar a kasar Ghana.

Har yanzu dai ba a bayyana yadda sojoji za su tunkari kasar ba, da tsawon lokacin da za a dauka, da kuma idan da gaske ECOWAS din za ta mamaye Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.