Isa ga babban shafi

An kaddamar da yakin zaben ‘yan majalisun Nijar mazauna kasashen waje

Masu sha’awar shiga takarar zaben ‘yan majalisun da zasu wakilci ‘yan Nijar mazauna kasashen waje sun kaddamar da yakin neman zabe a jiya Asabar 3 ga watan yuni na shekarar 20213 kamar yadda Hukumar zabe ta bada umarni. 

Kadamar da yakin zaben yan majalisun Nijar mazauna kasashen waje
Kadamar da yakin zaben yan majalisun Nijar mazauna kasashen waje © rfi hausa
Talla

A ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2023 ne shugaban kasar, Mohamed Bazoum, ya sanya hannu a dokar shirya zaben 'yan majalisun dokoki na yanki na 9 na kasashen waje. 

A karkashin wannan dokar, za a shirya zaben ‘yan majalisar dokokin kasashen waje a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni na wannan shekara ta 2023. 

A wasu kasashe da suka haka da Najeriya da Kamaru da Togo da Benin da kuma Cote D’Ivoire, jam’iyun siyasa kama daga masu mulki da ‘yan adawa sun shirya gangami na shiga yakin neman zaben tun daga jiya asabar, kuma’za a kuma kawo karshen yakin neman zaben ne a ranar Juma’a 16 ga watan Yuni na wannan shekarar. 

Hukumar zabe ta sanar da yiwa ‘yan Nijar 227,289 rajista a kasashe 15 dangane da wannan zabe. 

Yan Nijar zasu zabi yan majalisu guda biyar da zasu cike gurbi daga 171 da ake da su a yanzu haka a zauren majalisar dokokin kasar. 

Tun a shekara ta 2021 ya kamata a gudanar da wannan zabe, amma bulluwar annobar Covid 19 a wancan lokaci ya sa aka dage zaben zuwa wannan lokaci. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.