Isa ga babban shafi
Nijar

Jamhuriyyar Nijar na shirin kafa tarihin Demokradiyya

Jamhuriyyar Nijar na shirin kafa tarihi a Lahadi mai zuwa, inda al’ummarta za su fita rumfunan zabe don kada kuri’a a, zaben da zai zama irinsa na farko da za a mika mulki daga farar hula zuwa farar hula bisa turbar demokrdiyya a tarihin kasar, duk da barazanar tattalin arziki da kuma hare-haren ‘yan bindiga.

Wasu jami'an hukumar zaben Nijar CENI.
Wasu jami'an hukumar zaben Nijar CENI. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Nijar wadda Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana ta a matsayin kasa mafi talauci a yankin Sahel, ba ta taba zabar shugaban kasar da ya karbi mulki daga hannun zababben shugaban farar hula ba, tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa shekaru 60 da suka gabata.

Tun gabanin fara gangamin yakin neman zaben, shugaba mai ci Mahamadou Issoufou ya sha alwashin mika mulki salin alin ga duk wanda ya yi nasara a zaben.

Juyin mulki na baya-bayan nan da aka gani a Nijar shi ne na 2010 kusan shekaru 11 da suka gabata wanda aka hambarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Tandja Mammadou, shugaban da ya koma ga mahaliccinsa watanni 2 gabanin zaben na Lahadi mai zuwa.

Cikin kalaman shugaba Issoufou ga majalisar kasar, ya ce fatansa mika mulki ga zababben shugaban farar hula don tabbatar da dorewar demokradiyyar kasar ta Nijar.

Tuni dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yaba da kokarin shugaba Issoufou tare da bayyana shi a matsayin jigo ga Demokradiyyar kasar, yayinda ministan harkokin wajen Faransar Jean-Yves Le Drian ya bayyana yiwuwar zaben na lahadi ya zama zakaran gwajin dafi a nahiyar Afrika baki daya.

A cewar Emmanuel Macron yana da yakinin za a gudanar da sahihin zabe a kasar ta Nijar.

Jamhuriyyar Nijar dai na jerin kasashen yankin Sahel da ke fuskantar matsalar tsaro baya ga karuwar ayyukan ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.