Isa ga babban shafi
Afrika

A Nijar,sabon salon yakin neman zabe

Yayinda ake Shirin rufe yakin neman zabe a Nijar ranar Juma’a 25 ga watan Disamba 2020, a karon farko yan takarar shugabancin kasa da na yan majalisar dokoki sun fitar da wani sabon salo na bi kofa kofa, gida gida don neman kuri’un jama’a.

Yan siyasar Nijar
Yan siyasar Nijar
Talla

Yan takara 7 daga cikin 30 dake neman maye gurbin shugaban kasa Issofou Mahammadou suka shigar da kara kotu inda suke bukatar ganin ta haramtawa Bazoum takara, amma kuma kotun tayi watsi da bukatar su.

Daga cikin wadannan Yan takara akwai tsohon shugaban mulkin soji Janar Salou Djibo da Amadou Boubacar Cisse da Ibrahim Yacouba da Omar Hamidou Tchiana.

Sauran sun hada da Hamissou Mahaman Moumouni da Mamadou Moustapha Mamadou da Aboulkadri Alpha Oumarou da kuma Djibrilla Bare.

A ranar 17 ga wannan wata ne kotun tayi watsi da wannan zargi, matakin da ya tabbatar da sahihancin takarar Bazoum a karkashin Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.