Isa ga babban shafi
Afrika

Takarar Bazoum ta raba kań Yan siyasar Jamhuriyar Nijar

Yayin da ya rage mako guda a gudanar da zaben shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, batun takarar Bazoum Muhammad daga Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki na cigaba da rarraba kan al’ummar kasar saboda zargin da ake masa na cewa shi ba ‘dań kasa bane duk da watsi da zargin da kotun fasalta kundin tsarin mulki tayi. 

Dan takarar neman kujerar shugaban kasa a Nijar Bazoum Mohammed karkashin Jam'iyya mai mulki ta PNDS.
Dan takarar neman kujerar shugaban kasa a Nijar Bazoum Mohammed karkashin Jam'iyya mai mulki ta PNDS. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Yan takara 7 daga cikin 30 dake neman maye gurbin shugaban kasa Issofou Mahammadou suka shigar da kara kotu inda suke bukatar ganin ta haramtawa Bazoum takara, amma kuma kotun tayi watsi da bukatar su.

Daga cikin wadannan Yan takara akwai tsohon shugaban mulkin soji Janar Salou Djibo da Amadou Boubacar Cisse da Ibrahim Yacouba da Omar Hamidou Tchiana.

Sauran sun hada da Hamissou Mahaman Moumouni da Mamadou Moustapha Mamadou da Aboulkadri Alpha Oumarou da kuma Djibrilla Bare.

A ranar 17 ga wannan wata ne kotun tayi watsi da wannan zargi, matakin da ya tabbatar da sahihancin takarar Bazoum a karkashin Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki.

Kafin dai wannan lokaci Bazoum Muhammed ya rike mukamai da dama a Jamhuriyar Nijar cikin su harda na ministan harkokin waje da na cikin gida kafin ya sauka domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.