Isa ga babban shafi
Nijar

Al'ummar Nijar na kada kuri'a a zaben kananan hukumomi

Yau Jamhuriyar Nijar ke gudanar da zaben kananan hukukomi, wanda zai share faren zaben shugaban kasar da zai gudana ranar 27 ga wannan wata, zaben da zai kawo harshen mülkin shugaban kasa Mahamadou Issofou.

Wasu mata akan layin kada kuri'a yayin zaben kananan hukumomi da ke gudana a Jamhuriyyar Nijar.
Wasu mata akan layin kada kuri'a yayin zaben kananan hukumomi da ke gudana a Jamhuriyyar Nijar. Issouf Sanogo/AFP/Getty Images
Talla

Rahotanni sun ce an samu fitowar mutane da dama a sassan kasar kamar yadda wata jami’ar zabe Salima Salifou ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa a makarantar Dan Zama Koira da ke Birnin Yammai.

Akalla mutane kusan militan 7 da rabi suka yi rajistar zaben na bana, inda ake saran su zabi kansiloli a mazabu 266, zaben da aka kasa gudanar da shi tun daga shekarar 2016.

Rahotanni daga hukumar zabe sun ce mutane da dama basu samu damar yin rajistar ba a yankunan da ake fama da rikicin boko haram da kuma hare-haren 'yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ana saran Jam’iyyar PNDS da ke mulki ta samu nasarar lashe zaben tare da na shugaban kasa mai zuwa a zaben da zai zama irin sa na farko da zababben shugaban kasa zai mika mulki ga wani zababben shugaba a tarihin kasar.

PNDS ta tsayar da tsohon ministan cikin gida Bazoum Muhammed a matsayin dań takarar ta, yayinda kotu ta haramtawa babban dań adawa Hama Amadou tsayawa takara saboda samun shi da laifin safarar yara da kotu ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.