Isa ga babban shafi
Nijar

Shugaban Nijar ya samu ganawa da yan Nijar a Faransa

Mahamadou Issifou Shugaban Jamhuriyar Nijar dake halartar taron Duniya kan yanayi a borni Paris dake Faransa ya samu ganawa da yan Nijar mazauna kasar.A wanan ganawa yan Nijar mazauna Faransa sun bayyana fatar gani an cimma zaman lahiya mai dorewa tsakani  kabilu kasar.

Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou da yan Nijar a birni Paris
Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou da yan Nijar a birni Paris
Talla

Shugaba Mahamadou Issifou da babbar murya ya tabbatar da cewa zai bada cikkaken hadin kai zuwa  jam'iyyoyin siyasa dama hukumar zabe don gani an gudanar da zabeb kasar cikin kwantiar hankali da lumana,a daya wajen yayi gargadi zuwa yan siyasa da su kaucewa tada rikici.

Ya kuma bayyana matsayar kasar Nijar  dangane da wanan taro na Paris,Nijar na daga  cikin kasashen Duniya dake fatar gani  an dau matakan da suka dace domin tilastawa mayan kasashen Duniya biyan kudaden da suka dace .

A karshe Mahamadou Issifou ya gargadi yan Nijar mazauna kasashen Turai da su kaucewa duk wani abinda zai haifar da tarzoma ko rikicin adini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.