Isa ga babban shafi
Nijar

Hukumar zaben Nijar ta amsa kura-kurai a rijistar zabe

A karon Farko hukumar zaben Jamhuriyar Nijar ta amince da samun kura-kurai a rajistar masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da za a gudanar a watan Fabrairun 2016.

‘Yan adawar Nijar sun dade suna korafi kan yadda aka gudanar da rajistar zaben kasar
‘Yan adawar Nijar sun dade suna korafi kan yadda aka gudanar da rajistar zaben kasar AFP PHOTO/BOUREIMA HAMA
Talla

Hukumar ta fadi haka ne bayan zanga-zangar ‘Yan adawa na neman a soke rijistar saboda kura-kurai tare da zargin gwamnati da yunkurin yin magudi a zaben.

Sabiou Gaya, mataimakin shugaban hukumar zaben ya tabbatar da cewar lallai an samu kura-kurai a rajistar da suka hada da sunayen masu zabe da kuma salwantar wasu mazabu.

Ana saran hukumar zaben ta kammala gyara kura-kuran nan da ranar 22 ga wata.

‘Yan adawar kasar sun dade suna korafi kan yadda ake gudanar da rajistar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.